Zaben Edo: Jami’an tsaro sun hada baki da APC – Dokpesi
– Wani mai neman kujerar shugabancin PDP; Raymond Dokpesi yace APC tayi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben Jihar Edo
– Dokpesi yace ‘Yan Sanda sun kyale tsageru sun sace akwatunan zabe
– Fitaccen dan siyasan, ya zargi Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar da neman kama sa
Rikakken dan siyasar Jam’iyyar PDP dinnan, Raymond Dokpesi yace Jami’an tsaro sun taimakawa Jam’iyyar APC mai mulki wajen murde zaben da aka yi a Jihar. Raymond Dokpesi ya kuma yi kaca-kaca da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar saboda umarnin da ya bada na a kama sa. Raymond Dokpesi yace Jam’iyyar APC ta hada kai da ‘Yan sanda wajen sace akwatunan zabe.
Dokpesi ya bayyanawa Jaridar Punch cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar ya nemi da a kama sa, saboda tashin hankalin da ya faru a Garuruwan Agenobode, da Etsako.
Raymond Dokpesi yace shi dai kuri’a kurum ya dangwala yayi tafiyar sa, amma ake nema a kama sa da sunan ya tada rikici a zaben. Raymond Dokpesi ya kira Sufeta-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da ya gargadi Kwamishinan Jihar Edo.
KU KARANTA: Ana zaben sabon Gwamna a Jihar Edo
Dokpesi ya bayyana cewa an yi zabe lafiya lau, sai dai a wasu wurare an samu ‘yan bata-gari sun sungume akwatunan zaben. Dokpesi ya kuma tabbatar da cewa an yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a wurin zaben. Yanzu haka dai sakamakon zaben na ta fitowa daga bakin Hukumar zabe ta Kasa INEC, sun kuma nuna cewa dan takarar APC ne kan gaba.
Sakamakon zaben da suke fitowa daga bakin Hukumar zabe ta Kasa mai zaman-kan ta watau INEC sun nuna cewa dan takarar APC, Godwin Obaseki ne ke kan gaba, har yanzu a zaben. Sakamakon zaben da ya fito daga bakin ita kan ta Hukumar zabe ta Kasa, INEC sun tabbatar da cewa Godwin Obaseki ya samu nasara a Karamar Hukumar Igueben, da Egor, da Owan ta Yamma da kuma karamar Hukumar Uhunmode.
The post Zaben Edo: Jami’an tsaro sun hada baki da APC – Dokpesi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
