Zaben Edo: Jami’an tsaro sun zagaye ofishin INEC
An jibge jami’an tsaro daga rundunoni daban daban a ofishin hukumar zaben ta kasa na jihar Edo yayin da ake kirga kuri’un da zaben gwamnan jihar daya gudana a jiya laraba 28 ga watan satumba.
Yawancin jami’an tsaron sun fito ne daga rundunar yansanda, da yansandan kwanakwana sai kuma jami’ai daga rundunar tsaro ta farin kaya dauke da makamai. Bugu da kari akwai jami’ai daga rundunar sojan kasa.
KU KARANTA: Ginin makaranta ya ruguje a Legas
Gayyatan jami’an tsaron baya rasa nasaba da rahotannin hare hare da aka samu a wasu sassan jihar a ranar laraba, sa’annan an samu labarin kwacen akwatin zabe a wasu rumfunan zabuka.
Sai dai jam’iyyar PDP tayi ikirarin jam’iyyar APC tayi shirin aikata magudin zabe a sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi, mai magana da yawun jam’iyar Prince Dayo Adeyeye ya zargi APC da shirin yin magudin zabe, ta hanyar amfani da gwamna Adams Oshiomole.
The post Zaben Edo: Jami’an tsaro sun zagaye ofishin INEC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
