Dan Majalisan da aka dakatar, Jibrin ya maida martani
– Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Tarayya, Abdul Jibrin ya bayyana cewa har yanzu yana kan bakan sa
– Dan Majalisan da aka kora, Hon. Jibrin yace tabbas Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara yayi awaon gaba da wasu kudi daga cikin kasafin bana
– Hon. Jibrin yace ba zai ba da hakuri ba, don bai yi laifin komai ba
Hon Abdulmumin Jibrin
A jiya da rana ne Majalisar Wakilai ta Tarayya ta tsige Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Hon. Abdulmumuni Jibrin wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji na Jihar Kano. Majsalisar dai ta dauki wannan mataki ne bayan da Hon. Jibrin ya ki amsa gayyatar wani kwamitin gudanar da bincike. Hon. Jibrin ya zargi Shugaban Majalisar wakilan Kasar, Dogara Yakubu da laifin handame wasu kudi daga kasafin bana.
Sai dai Majalisar ta dakatar da shi daga aikin zaman Majalisar na lokacin da ya kai rabin shekara, haka nan kuma, an haramta masa rike wani matsayi a Majalisar har karshen wa’adin wannan Majalisar watau zuwa Shekarar 2019. A baya dai Jibrin ya rike mukamin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi a Majalisar, kafin a tsige sa kafin Majalisar ta tafi hutu a watannin baya kadan. Haka kuma Jibrin ya taba rike Kwamitin kudi a Majalisar, inda a wancan Gwamnatin, ya jefa tambayoyi hamsin ga Ministan Kudin Kasar, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.
KU KARANTA: An dage karar Saraki da su Ekweremadu
Haka kuma Majalisar na neman Hon. Jibrin din ya bada hakuri saboda bata mata suna da yayi, sai dai Hon. Jibrin yace sam bai yi laifin komai ba, kuma ba zai bada hakuri ba. Hon. Jibrin ya tabbatarwa BBCHausa cewa tabbas Shugaba Dogara da wasu manyan ‘yan majalisar, sun yi kokarin awon gaba da Naira Biliyan 30 daga cikin kasafin kudin bana. Ya kara da cewa Shugaba Dogara da kuma Mataimakin sa Yusuf Lasun, da wasu manya a Majalisar sun yi gaba da wasu Naira biliyan 40 daga cikin kudin da aka ware na Majalisar, Naira Biliyan 100.
Hon. Jibrin dai tuni ya garzaya Kotu da Lauyan sa, Femi Falana yana kalubalantar korar sa da aka yi. A wannan lokaci dai Jibrin bai da damar zuwa kusa da Majalisar ko kuma karbar albashin sa da alawus.
The post Dan Majalisan da aka dakatar, Jibrin ya maida martani appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
