Kungiyar OPEC za ta rage hako man fetur
– Kungiyar Kasashe masu fita da danyan mai a duniya watau OPEC ta dauki matakin rage yawon man da ta ke hakowa
– Kungiyar OPEC za ta rage yawon hako man fetur din ne domin farashin man ya kara daraja a kasuwa
– Kawo yanzu haka, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu
Gidan jaridar Al Arabiya ta rahoto cewa Kungiyar Kasashen duniya masu mai-OPEC ta dauki wani gagarumin mataki na rage yawan danyen man da ta ke hakowa a duniya. Kungiyar Kasashe masu arzikin man sun dauki wannan mataki ne domin farashin gangar danyan man ya daga a kasuwannin duniya, wanda ya fadi war-was cikin shekarun bayan nan.
Wannan ne dai karo na farko cikin shekaru kusan 8 da Kasashe masu arzikin man duniya za su dauki irin wannan mataki. Wannan mataki ya zama dole ne dai bayan da farashin man ya ruso Kasa cikin kwanakin nan. Kungiyar OPEC din ta yanke wannan mataki ne a wani taro da tayi a Kasar Algeria.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da ministoci
Kasar Najeriya na fama da matsala sanadiyar faduwar farashin man fetur din a Kasuwannin duniya, bugu da kari kuma tana shan barna daga tsagerun yankin Neja-Delta, inda man Kasar yake. Haka ma Kasashen da suka dogara da man fetur din suke ta kokawa, irin su – Saudiyya, da kuma uwa-uba Kasar Venezuela.
Ana dai sa ran wannan yarjejeniya ya sa farashin su daga, kawo yanzu ma dai, BBC ta rahoto cewa har kudin man na fetur ya kara kudi a Kasuwannin duniya da kusan kaso 6%, haka kuma hannun jari a Kasuwannin.
The post Kungiyar OPEC za ta rage hako man fetur appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
