Shin yan kungiyar Boko Haram sune makiyaya masu kisa? Sojoji sunyi kamu mai girma (hotuna)
– Sojoji sun kama wasu yan ta’adda da sukayi kokarin shiga kasuwar dabbobi a jihar Borno
– An kuma kama dan leken asirin kungiyar Boko Haram dake boye a kasuwar
– Wani dan ta’adda ya zo siyar da shanaye ya kuma yi shirin amfani da kudin kan ci gaba da kai harunsu
Da ala zaton da akeyi na cewa abubuwan yan kungiyar Boko Haram na shige da makiyaya ya fara zama gaskiya kamar yadda jami’an sojoji suka kama wasu yan ta’adda a kasuwar dabbobi.
A sanarwa daga Kanal Kukasheka Usman wadda shine kakakin sojoji, ya ce an kama yan ta’addan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba a kasuwar dabbobi a jihar Borno.
KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya shawarci Buhari kan kudin Abacha
An kuma kama wani Alhaji Ajib Umar wadda aka bayyana a matsayin dan leken asirin yan ta’addan don ya amsa tambayoyi.
Karanta cikakken labarin a kasa:
A safiyar ranar Laraba a kasuwar dabbobi, dake Maiduguri, jihar Borno, rundunar sojoji na Lafiya Dole tare da taimakon yan farar hular JTF, sun kama mutane 3 da ake zargin yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne.
Kasuwar Dabbobi
Wadanda ake zargin sun hada da Abba Go Dallagio, Abba Fanned da kuma Alhaji Nwariye. A lokacin bincike na sharar fage sunyi ikirarin cewa sun jigo garin Maiduguri ne ta Mafa tare da kimanin shanaye 200 na siyarwa a kasuwar dabbobin Maiduguri.
KU KARANTA KUMA: Najeriya ta fita daga koma bayan tattalin arziki
Wadanda ake zargin sun ci gaba da bayyana cewa suna daga cikin masu dabarun aikin yan ta’addan kungiyar Boko Haram cewa suna taimakawa gurin siyar da shanaye nay an ta’addan.
Sun kara da cewa suna kai way an ta’addan kudi don ci gaba da ayyukansu, rundunar sojoji sun gano sun kuma ware shanaye 23 a kasuwar dabbobin.
Shanaye
Haka kuma, an kama daya daga cikin yan leken asirinsu a kasuwar, Alhaji Ajid Umar. An ware kimanin shanaye 170 dake da nasaba da shi. Dukkan wadanda ake zaregin na fuskantar binciken sharen fage.
The post Shin yan kungiyar Boko Haram sune makiyaya masu kisa? Sojoji sunyi kamu mai girma (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
