Abun al’ajabi! Najeriya ta riga ta fara fita daga koma bayan tattalin arziki cewar Minista
-Ministan kudin Najeriya, Kemi Adeosun ta bayyana cewa koma bayan tattalin arziki ya kusa zama labari
-Mrs Adeosun tace saura kiris kasar ta fita daga koma bayan tattalin bayan sanya baki na musamman daga gwamnatin tarayya
-Adeosun ta ce ana sa ran gwamnati zata kara kaimi don dawo da kasar zuwa ga tsohon daukakarta
Ministan kudi Kemi Adeosun
Mrs Kemi Adeosun ta bukaci yan Najeriya da su kasance cikin kyautata zato, ta jaddada cewa kasar ta kusa fita daga koma bayan tattalin arziki.
Ministan kudi, a ranar Laraba 29 ga watan Satumba ta bayyana cewa kasar ta rigada ta fara fita daga koma bayan tattalin arziki, cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakan da suke da amfani don yan kasar.
KU KARANTA KUMA: Oshiomhole yayi nasara a mazabar sa
A cewar jaridar Vanguard, Adeosun ta bayyana hakan a gurin taron kwanaki biyu da ta shirya na kungiyar kudade na kasa da ci gaban tattalin arziki wato National Council of Finance and Economic Development (NACOFED) a garin Abeokuta.
Adeosun ta bukaci dukkan kwamishinonin kudi na dukkan jiha, akawu janar da dukkan kwararru a fannin kudi, da su yi lissafin a takardun su, cewa zai taimaka masu gurin yanke shawara.
Ta yi bayanin cewa yunkurin zai bari jihohin su san wajibobin su, karfi da kuma hanyar da zasu bi da kudadensu a nan gaba, ya kara da cewa zai taimaka sosai ga gwamnatin tarayya.
The post Abun al’ajabi! Najeriya ta riga ta fara fita daga koma bayan tattalin arziki cewar Minista appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
