Shin wai yanzu karuwai suna bada rasit ne idan aka biya kudin yin amfani dasu?
Da alamun dai karuwai yanzu sun kara wani sabon tsari a harkar kasuwan cin su, inda suka kara bullo da wasu sabbin abu domin kara daukar sana’ar nasu da kyau.
Idan kuka duba hoton nan dake kasa, zaku gane cewar karuwai yanzu sun dauki wasu sabbin salo domin kara kayatar da sana’ar nasu.
A cewar hoton da aka gani wanda ya watsu a yanar gizo, ya nuna cewar karuwan suna bayar da rasit ga masu kwanciya dasu domin su masu mu’amalan dasu su tabbatar da cewar sun dauki sana’ar nasu da mahimmanci.
KU KARANTA: Tirkashi! Kallin jerin sunayen gwanayen yan wasan UEFA
A yanda rasit din ya nuna, ya bayyana wata mata mai sana’ar karuwanci wanda ake kira da suna Millicent Wambui, inda ta caji abokin harkar nata mai suna Joseph Kamau, 500 duk minti daya. Inda suka shirya jinga akan awa biyu zaiyi, wanda kudin ya kama 60,000. Ga dai rasit din nan a kasa.
Allah ya kyauta!
The post Shin wai yanzu karuwai suna bada rasit ne idan aka biya kudin yin amfani dasu? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
