Wata mata ta banka wa mijinta wuta, sannan wannan ya faru (hotuna)
Wata fusatacciyar mata na cikin matsala a yanzu kan ta banka wa mijinta da kaninsa wuta bayan sun samu sabani.
Wata Mata mai shekaru 38 da aka kira da Comfort Agboloshie, ta jika wasu kaya a cikin kananzir, tana yin hadaddiyar giya, wanda ta jefa a dakin da mijinta da kaninsa ke bacci.
Comfort ta babbaka mijinta da sirikinta da wuta
Ko da dai mijinta mai shekaru 45 Lawrence Nkem ya rayu, kaninsa mai shekaru 42 Benjamin Oyem, ya rasa ransa a asibiti inda akayi gaggawan kaisu bayan mugun kuna da kuma raunuka da ya samu sakamakon wutan.
KU KARANTA KUMA: Olonishakin yayi shellar yan Boko Haram 50 da ake nema
A halin yanzu ba’a san dalilinta mna aikata wannan danyen aiki ba, an rahoto cewa Comfort tayi nazari sosai kafin ta gudanar da shirinta, kamar yadda aka ce sai da ta kwashe yayanta guda uku daga dakin kafin afkuwar al’amarin a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba.
Allah ya kyauta da irin wannan mata!
The post Wata mata ta banka wa mijinta wuta, sannan wannan ya faru (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
