Dumi-dumi: Bola Tinubu bai da lafiya
– Ashe rashin lafiya ce ta hana Bola Tinubu fita gangamin APC, inji wani gwamna
– Gwamnan jihar Plateau yace duk wadanda ba su halarci gangamin neman zaben jihar Ondo ba sun bada uzuri
– Gwamna Simon Lalong ya nuna cewa babu wani rikici a jam’iyyar APC
Shugaba Buhari
Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya bayyana dalilan da suka hana Manyan ‘Yan APC musamman na bangaren Kasar Kudu maso Yamma halartar gangamin yakin neman zaben Jihar Ondo da aka yi a karshen wannan makon.
Gwamna Simon Lalong yace duk wadanda ba su halarci taron ba, sun ba da hakuri tare da bada uzurin da ya hana su zuwa. Gwamna Lalong din shine Shugaban Kwamitin Yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Ondo, ya bayyana haka a Garin Abuja.
KU KARANTA: Gwamnonin da Tinubu zai balle da su
Lalong yace rashin kafiya ne ya hana Bola Tinubu zuwa taron, Gwamnan kuma yace suna masa addu’a ya samu sauki. Yace ba matsala bane don Bola Tinubu bai je ba, tun da ba ya jin dadi, haka kuma dai Shugaban Kasa da Shugaban Jam’iyya duk sun halarta.
Gwamna Lalong ya godewa Shugaba Buhari da kokarin da yayi na zuwa Garin Akure domin tallata dan takarar APC din. Gwamnonin Legas, Oyo da Osun dai ba su halarci gangamin ba.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Dumi-dumi: Bola Tinubu bai da lafiya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
