Ba za mu ba da damar da siyasa zatayi tasirin raba mu ba- gwamnonin Yarbawa
– Gwamnonin jiha a yankin kudu maso yammacin Najeriya sunyi nufin kirkiran alkibila daya
– Hadewar kan yanki shine na farko a ajandar gwamnonin Yarbawa
– Sun kuma yanke hada kai gurin hana yan waje shiga lamarunsu wand aka iya haifar da wahalhalu a tattalin arzikin yankin da kuman amfanin al’ummar su
Gwamnonin jiha a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sunyi nufin kirkiran alkibila daya a kokarinsu na hana abubuwan da ka iya shigowa daga waje don dukufar da tattalin arziki da kuma al’umman yankin.
Gwamnonin sunyi alkawarin a jiya, 21 ga watan Nuwamba bayan wani taron tattalin arziki da gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya shirya a majalisa a garin Ibadan.
A wata sanarwa da gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yayi a karshen taron, ya kara nanata cewa akwai bukatar gwamnonin su yi amfani da hadin kan yankin don samar da maslahar tattalin arziki ga mutanen kudu maso yamma musamman a fannin koma bayan tattalin arziki dake sassa daban-daban na kasar.
KU KARANTA KUMA: Wata mata ta banka wa mijinta, kanin mijinta wuta a Ghana
Fayose ya sanar da manema labarai cewa gwamnonin sun tattauna a kan matakai da ya zama dole a dauka don inganta ci gaba a yankin da kuma gabatar da hanyar da yafi dacewa kan bawa talaka abinci.
Yace gwamnonin na kula game da dangantakarsu ta fannin tarihi da kuma salsalar inda suka fito, duk kuwa da bambancin siyasarsu.
The post Ba za mu ba da damar da siyasa zatayi tasirin raba mu ba- gwamnonin Yarbawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
