Kungiyar kwadago ma ta soki tsarin tattalin arzikin shugaba Buhari
Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Soki tsarin tattalin arzikin gwamnatin Buhari inda ta bayyana cewa tsarin bai dace da ma’aikata a matsayin wani matakin na samun sauki daga halin kuncin da ake ciki a yanzu.
Shugaban Kungiyar Kwadagon, Ayuba Wabba ne ya yi wannan ikirarin inda ya nuna cewa rashin biyan albashi da alawus alawus na ma’aikata ya sanya sun fi kowa shiga kunci a wannan lokaci yana mai cewa har yanzu gwamnati ba ta gano bakin zaren ba.
Ya ce matakan da gwamanti ta dauka na rage darajar Naira, kara kudin fetur da haraji duk ba su tasiri ba. Ya kuma zargi gwamnati da makarkashiyar dakile batun karin albashi da kungiyar ta gabatar mata.
The post Kungiyar kwadago ma ta soki tsarin tattalin arzikin shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
