Majalisar Amintattun PDP sun mayar da taro Abuja
–Gwamna Nyesom Wike ba zai jagoranci kwamitin shiriya taron gangamin jam’iyyar PDP ba.
–Majalisan Amintattu sun ce ma kwamitin rikon kwarya karkashin sanata Ahmed Makarfi cewa su nada sabuwar kwamitin shirya taron gangami
–Majalisan amintattun sun nuna amincewansu ga shugabancin kwamitin rikon kwaryan.
Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ta nemi kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar karkashin ahmed makarfi da ta nada sabuwar kwamitin shirya taron gangamin ta .
Ta fadi hakan ne domin tabbatar da cewa an gudanar da taro cikin zaman lafiya da lumana. An bayyana hakan ne bayan ganawar da majalisan tayi a ranan litinin, 29 ga watan agusta Musa Yar,Adua Center, Abuja.
Shugaban majalisan amintattun, Sanata Walid Jibrin ,wanda ya jagoranci ganawar yace za’a yi taron gangamin jam’iyyar na gaba a babban birnin tarayya Abuja. Majalisan sun nuna amincewansu ga kwamitin rikon kwarya da kuma farin cikin su ,kana suna kira dasu cewa su cigaba da ayyuka mai kyau domin kawo sauyi jam’iyyar.
A wata takarda da jibrin ya sa hannu, tace : “Majalisan amintattu zata hanzarta samar da kudi ga jam’iyyar. Kuma tana cigaba kokarin samar da hadin kai tsakanin bangarori maras jituwa. Kana ganawar na kira ga duka Gwamnonin jihar da su cigaba da shirye shirye domin nuna ma jama’a tashen jam’iyyar PDP. A karshe, Majalisan amintattu nabaiwa kwamitin rikon kwarya shawara cewan kwamitin ta gana da wuri domin zantar da manufofin jam’iyyar domin cigaba.”
KU KARANTA : Ana zargin Goodluck Jonathan da hannu cikin magudin zabe
Zaku tuna cewa taron gangamin PDP ta waste sau 2 a kasa,a fatakwal wanda aka ji kunya.
A ranar 21 ga watan mayu, an samu matsala ne yayinda aka cire shugaban jam’iyyar, Ali modu sherrif daga mulki. Daga baya aka shirya wani a ranan 17 ga watan Augusta karkashin jagorancin gwamna Nyesom wike a jihar ribas, Amma yan sanda suka hana yin taron saboda umurnin kotuna biyu masu tanakudi da juna.
The post Majalisar Amintattun PDP sun mayar da taro Abuja appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
