Sarkin Legas yayi tsokaci kan gwamnatin Buhari
A wata hira da Sarkin Legas Oba Rilwan Akiolu I yayi da gidan talabijin na Channels ya bayyana ra’ayinsa dangane da tafiyar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sarkin yace shugaba Buhari ba zai iya barin halinsa sojoji ba, sai kuma ya roki yan Najeriya da su kara hakuri.
Yace “dubi yadda Buhari ke kokarin farfado da kasarnan, yana da niyya mai kyau, sai dai kawai kasan tsohon soja ne, ya rigaya ya saba da halayyar soji. Amma muna sa ran abubuwa zasu yi kyau, mu kara hakuri.
“idan muka dage wajen baiwa Buhari goyon baya da shawarwari, abubuwa zasu canza. Shima fa dan adam ne, kuma dan adam tara yake bai cika goma. Manyan matsalolin dake damun kasarnan sune rashin aikin yi da tsaro. “amma idan gwamnatin ta dage, mu kuma muka cigaba da addu’a, da sannu zamu samu saukin matsalolin nan. zamu ji dadi, amma fa sai kowa ya bada gudunmuwa.
“a kwanakin baya na ji mataimakin shugaban kasa na cewa sun tara makudan kudade sakamakon daina biyan tallafin man fetur, don haka nake ganin ya kamata su yi kashe kudaden nan wajen taimaka ma marasa aikin yi, amma wani abin ban haushi da mutanen Najeriya shine mun fi so muyi sata, bamu son yin aiki, shi kuma Buhari ba zai yadda da sata ba.”
Basaraken ya kara nanata soyayyarsa ga kyawawan mata. Akiolu ya bayyana cewa ya kwashe shekaru 56 yana addua’an zama Sarki. “tun a shekarar 1964 nake rokon Allah yasa in zama Sarki, bayan rasuwar Sarki Adele. Ina cikin kwallo ne naga jama’a na dauke da kankara, sai na taya su dauka, ban san me ke faruwa ba, sai kawai washegari naga jaridu na dauke da hotunan mu”
“daga nan ne na fara addu’ar zama Sarki. Ina da kokarin neman kudi, kuma na iya kashe kudi, sa’annan ina son kyawawan mata, babu yadda aka iya dani, haka nake”
A ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2003 ne aka rantsar da sarki Rilwan Osuolale Akioulu a matsayin sarkin Legas. Matansa hudu a lokacin da ya zama sarki, ciki har da yar sarkin Owo n jihar Ondo.
The post Sarkin Legas yayi tsokaci kan gwamnatin Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
