Ya nemi auren budurwarsa da kyautan mota
Wani dan saurayi ya sanya yan matan Najeriya shiga yanayin tsananin kishi bayan ya baiwa budurwarsa kyautan wata tsaleliyar mota.
Kamar yadda dan saurayin ya bada labara a shafinsa na Twitter, yace ya baiwa budurwar tasa kyautan mota kirar Camry ne sakamakon amincewa da tayi ta aure shi.
Wannan lamari ya afku ne a gaban dakunan kwana na yan mata dake jami’ar jihar Legas mai suna Moremi Hall, wanda yaja hankalin mutanen dake wajen, inda wasu kuma suka yi musu addu’ar fatan alkhairi.
Ga yadda abin ya kasance dai: “wani dang aye ne ya ajiye wannan motar a gaban Moremi Hall, inda ya sanya mata lamba kamar haka ‘Nagode da kika amsa min’.
The post Ya nemi auren budurwarsa da kyautan mota appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
