An tsare Diego Maradona bayan an kama sa da fasfon bogi
– An tsare gwarzon kwallon kafar nan Diego Maradona a Birnin Buenos Aires bayan an kama sa da fasfon bogi.
– Tsohon dan wasan Kasar na Argentina yana shirin zuwa Dubai kenan shi da mai dakin sa.
– Maradona dai ya bayyana wadanda suka jefa sa cikin wannan abu.
An tsare gwarzon dan wasan kwallon kafar duniyar nan Diego Maradona a Birnin Buenos Aires, babban birnin Argentina, bayan an kama sa da takardun jabu.
An kama tsohon dan wasan na Kungiyar Napoli ne a Babban Birnin Kasar na Argentina a daren ranar Lahadin nan, Jami’an dai sun kama sa ne bayan an same sa da takardun fasfo na bogi. Kafar ‘Euro sports per reports’ Ta Argentina ta rahoto wannan labari.
Diego Maradona ya shirya zai bar Kasar ne zuwa Birnin Dubai tare da iyalin sa, Rocio Oliva, sai dai Jami’an sufuri da ‘yan sanda sun tsare sa, da sunan yana yawo da takardun sata. Maradona dai bai samu tafiya a wannan jirgi ba, hakan ta say a kira lauyan sa, har aka sake sa.
A cewar Diego Maradona dai abin da ya faru ba ya rasa nasaba da siyasa. Maradona yace: “Ba zan fa bari wani ya tsara mani rayuwa ta ba, shekaru 15 da suka wuce, babu wanda ya isa ya fada mani ga abin da za nayi…Batun ace na sato takardu wannan shirmen banza ne!” Maradona ya kara da cewa: “Lauya na zai binciki wannan lamari da ‘yan siyasa suka jefa ni ciki”
KU KARANTA: AN HADA DURON UEFA CHAMPIONS LEAGUE
Diego Maradona na daga cikin gagaruman ‘yan wasa da aka taba yi a tarihi, tare da su Pele na Kasar Brazil, har wasu ma suna ganin cewa dan wasan ya zarce kowa a duniya wajen taka ledar. Ya bugawa Kungiyoyi da dama, ya; Boca Juniors, Napoli, Sevilla da kuma Barcelona.
The post An tsare Diego Maradona bayan an kama sa da fasfon bogi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
