Gasar Olympics: Brazil ta dauki gwal a wasan kwallon kafar maza
– Kasar Brazil ta samu cin lambar gwal a wasan kwallon kafar maza na Gasar Olympics.
– Brazil ta doke Kasar Jamus a bugun finariti.
– Wannan ne karo na farko da Kasar ta samu wannan kyauta a tarihi.
Kasar Brazil ta samu cin lambar gwal a wasan kwallon kafar maza a Gasar Olympics RIO 2016 bayan ta doke Kasar Jamus a bugun finariti. Dan wasa Neymar ya fara cin kwallo a wasan.
Kasar Brazil ta samu lashe gwal a wasan kwallon kafar maza na U23 na duniya a Gasar Olympics RIO 2016. Dan wasan nan na Barcelona kuma Kyaftin din Brazil din Neymar yaci wata ‘firinkit’ a minti na 27, wannan abu ya kidimar da ‘yan kallon da ke filin wasan da ke Birnin Rio.
Ya kamata dai ace Brazil din ta kara kwallaye, sai dai Kasar Jamus din tana da kwararrun ‘yan baya. A minti na 59 ne Max Meyer ya zunduma wata kwallo a ragar ta Brazil, hakan ya sa aka samu yin kunnen doki, duk da cewa Brazil din sun fi rike kwallo a wasan, sai dai ba ta samu leka ragar na Jamus ba.
KU KARANTA: DALILIN DA YA SA AKA CIRE NAJERIYA A OLYMPICS
Haka yasa aka tafi zuwa bugun finariti watau bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida, Nils Petersen na Jamus ya gagara jefa ta sa finaritin a raga, Dan wasa Neymar kuwa yana zuwa ya doka ta sa har raga.
Jamus ce ta doke Najeriya da ci 2-0, haka kuma Brazil ta lallasa Honduras da ci har 6-0 a wasan kusa da karshe. Wannan ne dai karo na farko a tarihi da Kasar ta Brazil ta samu cin lambar gwal a wannan gasa. Najeriya kuma ta samu cin tagulle, inda Jamus ta samu kyautar zinariya a Gasar na Olympics.
The post Gasar Olympics: Brazil ta dauki gwal a wasan kwallon kafar maza appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
