Daliban jihar Kano a Sudan da India na cikin tsaka mai wuya
-Watanni 10 ke nan ba a biya su alawus-alawus ba
-Daliban sun gagara biyan wurin kwana da na abinci
-Gwamnatin jihar ta koka rashin kudi
Daliban da gwamnatin jihar Kano ta tura su karatu a kasar Sudan da Indiya sun kokaw da irin halin matsin da suke ciki na rashin kudi sakamakon kin aika musu da kudi da gwamnatin jihar ba ta yi ba har na tsawon watannin 9 zuwa 10.
Gwannan Kano Abdullahi Ganduje
A hirar da gidan Rediyon Rahma ya yi da wasu daliban da ke karatu a Sudan da kuma India, aka kuma saka a rahoto, Salmanu Gambo wani dalibi daga kasar Sudan wanda ke magana da yawun sauran dalibai a kasar ya ce, abincin da za su ci yana gagararsu ballantana abin da za su biya dakunan kwana, wanda hakan ke haifar da nakasu a karatunsu.
KU KARANTA: Kano ta sallami wasu ma’aikata saboda almundahana
Ita kuwa wata daliba mai suna Baraka daga Indiya cewa ta yi, sun shafe watanni 10 ba su ga ko kwabo ba daga gwamnati, ta kuma kara da cewa, ba su da kudin da za su sayi littafan karatu, ga kuma karatowar jarrabawa ga wadanda ke shirin kammala karatun nasu.
A hirar da aka yi da Ahmed Bature Garba, Darakta mai kula da al’amuran makarantu, wanda kuma ya yi magana a madadin Babbar Sakatariyar Hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar, ya ce, halin da daliban ke ciki na damun gwamnati, kuma ta na iya bakin kokarin ganin ta aika musu da kudadensu.
Kimanin ‘yan asalin jihar 360 ne ke karatun zama Likita a Sudan yayin wasu adadi mai yawa ke karatun harhada magunguna da kuma aikin Likita a Indiya.
The post Daliban jihar Kano a Sudan da India na cikin tsaka mai wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
