An gano wani saurayin likita a mace
-Wani saurayin likita ya bace tun ranar 24, ga Yuli 2016
-Dan mai gadi ya kashe shi da sara
-Wanda ake zargi ya gudu amma abokan laifinsa na hannun ‘yan sanda
An gano gawar wani mamba na kungiyar lokitocin Najeriya Dr Abdulkareem Tunde Abdulrahman, wanda aka ce ya bace. An sami gawar likitan a gidan mahaifinsa da alamar bugu da itace inda bincike ya nuna ya rasu wajen karfe 1:00 na safe ranar 24, ga Yuli, ranar da aka ce ya bata
Wanda ake zargi mai suna Jamiu Mohammed, da ne ga mai gadin gidan uban mamacin Lawya Abdulrahman Alarape Adeyi, wanda ke zaune a gida mai lamba 3, Parfesa Awe Close, Daga titin Abdulkareem Adisa, GRA, Ilorin. Jamiu dai ya tsere bayan aikata aikin ashsha tare da wasu mutane biyu wadanda ke hannun jami’an tsaro domin bincike
A cewar jaridar The Herald, wanda ake zargin, tsohon mai laifi ne tare da wasu sun afka ma likitan a dakinsa suka kashe shi da bugu. Yayin da mahaifin Wanda ake zargin ya nuna rashin sanin kisan har sai da aka kira jami’an tsaro kafin a sami wani jawabi daga gareshi, an sami wayoyin mamacin a hannun wasu mutane biyu wadanda ke amsa tambayoyi hannun jami’an tsaro kan dalilin, da yadda aka kashe Tunde Abdulrahman.
KU KARANTA : Mutane 16 sun kone kurmus a hadarin mota
Ana zargin jamiu da saka gawar mamacin a gidan kaya na motarsa ya kaita wani wuri da b’a sani ba. Ana zaton yayi kisan ramuwa ne domin mutuwar mahaifiyarsa wadda ta rasu dalilin cholera shekaru biyu da suka wuce, duk da taimakon da mahaifin mamacin ya bada wajen rufe ta
The post An gano wani saurayin likita a mace appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
