Gwamnan Kros Riba ya ladabtar da kwamishina kan latti
Gwamnan jihar Kros Riba Ben Ayade ya sallami kwamishinar ruwa na jihar Ntufam Gabe Odu Ojie kan laifin zuwa aiki latti.
Kazalika ya sallami manajan hukumar ruwa ta jihar Oju Igile shima akan latti.
A yayin da yake zantawa da yan jarida a farfajiyar ma’aikatan ruwa a kalaba, gwamnan yace “yanzu karfe 9, amma har yanzu kwamishinan ruwa bai iso wurin aiki ba. Ban san dalilin da ya hana shi zuwa aiki akan kari ba. Don haka na dakatar dashi. Zamu nada wanda zai amshi ragamar tafiyar da ma’aikatan. Duk wani kwamishina da na kama da irin laifinnan zai tafi.
Sanarwan sallaman nasu ya faru ne daidai lokacin da gwamna Ayade ke yawon rangadi na ba zato zuwa hukumomi da ma’aikatu don ya tabbatar da jami’an gwamnati suna bin dokokin aiki. A cewarsa, rashin da’a ne ace ma’aikacin gwamnati bai isa wurin aiki ba kafin karfe 9 na safe. Yace dakatarwar zata zamo izina ga sauran ma’aikata.
A satukan da suka gabata ne dai jam’iyyar hamayya a jihar APC ta yi kira da a tsige gwamna Ayade sabod keta kundin tsarin mulki da yake yi, da kuma dalilin matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar. Jam’iyyar tana zargin gwamnan da rashin tabuka komai wajen magance matsalolin da suka shafi lafiyar al’umma, kare rayukansu da kadarorinsu.
The post Gwamnan Kros Riba ya ladabtar da kwamishina kan latti appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
