Hukumar soja ta kyale wanda take nema ya koma gida
-Hukumar soja ta sallami Ahmed Bolori wanda take nema ya koma gidansa bayan ya kai kansa wajenta
-Bolori yayin zaman jira na awa biyu ba tare da an tuhumceshi ba kafin a sallameshi
-Wani na kusa da Bolori, Farouk Kperoogi yace ba dai dai bane hukumar ta nuna muhimmancin nemansa bayan ba haka bane
Awowi bayan hukumar soja tayi yekuwar nemansa, hukumar sojan Najeriya ranar Lahadi, 14 ga Agusta ta sallami Ahmed Bolori ya koma gida bayan ya kai kansa a wani sansani dake jihar Borno.
Ahmed Bolori, who was declared wanted by military
An yi yekuwar neman Bolori, shugaban wata cibiya dake la’antar tsagerancin tashin hankali ko kuma Fa’ash Foundation and the Partnership Against Violent Extremism, tare da wasu mutum biyu ranar Lahadi, amma an sallameshi ya koma gida yayin da ya kai kansa ga hukumar
Premium Times ta ruwaito wani na kusa da Bolori Farook Kperoogi, wani malamin nazarin aikin jarida kuma mazaunin Amurka ta shafinsa na Facebook na cewa Bolori ya gaya masa ya kai kansa “wani babban sansanin soja a Maiduguri, yayi zaman jira na awa biyu amma ba wanda yace masa uffan”
KU KARANTA : Iyayen yan matan Chibok sun fashe da kuka
Kperoogi, ya nuna rashin jin dadinsa da yadda hukumar soja ta kururuta nemansa, bayan ba haka bane. Yace Bolori “ya gaya mani cewa ya buga waya ga shugaban sojoji, da mai magana da yawun hukumar da ta ayyana “nemansa” da kuma wasu manyan jami’an soja cewa duk lokacin da suke bukatarsa zai kai kansa, ba sai ance ana “nemansa” ba, tunda ba a boye yake ba. Bayan haka sai ya kai kansa ga hukumar”
The post Hukumar soja ta kyale wanda take nema ya koma gida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
