PDP ta nunawa wani mai shari’a yatsa
-Jam’iyyar PDP ta nunawa wani mai shari’a kan yadda yayi kokarin hana babban taronta
-Wani babban ya ce taken-taken mai shari’ar ba su dace ba
-Wata kotu ta ba da umarnin a yi taron
Jam’iyyar PDP
Daya daga cikin masu neman takarar sakararen yada labari na jam’iyyar PDP, Deji Adeyanju ya bayyana abin da PDp ta shirya yi wa mai shariar da ya yi kokarin hana babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a fatakwal.
A cewar Adeyanju, jam’iyyar za ta aikawa da mai shari’ar gargadi mai karfin gaske a filin babban taron da za a gudanar a ranar Laraba 17 ga watan Agusta.
KU KARANTA: Kokawar kujerar shugabancin PDP ya kankama
A wani sako da ya lika a shafinsa a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter, a ranar Talata 16 ga wata, Deji, mai zawarcin kujerar shugabancin jam’iyyar, ya kuma ci gaba da cewa, “Abang na kunyata bagaren shari’ar kasar nan, kuma za mu yi masa gargadai mai karafin gaske a babban taron”.
Idan za a iya tunawa bangaren jam’iyyar a karkashin Ali Modu Shariff ne ya kai karar bangaren Ahmed Makarfi gaban wata babban kotun tarayya a Abuja a inda Sheriff din ya ke neman kotun da ta dakatar da babban taron na kasa.
KU KARANTA: Rikicin PDP Modu Shariff ya tubure
Saboda a cewarsa, shi ne kadai a matsayinsa na shugaban jam’iyyar da zai iya kira babban taron, kuma ba zai sauka ba sai shekrara ta 2018, don haka babbar kotun ta haramta taron. Babban Kotun a karakashin Mai shari ’a Okon Abang ta amince da rokon na Modu Shariff tare da jaddada matsayinsa na shugabancin jam’iyyar.
The post PDP ta nunawa wani mai shari’a yatsa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
